Alkalan wasa mata a fagen kwallon kafa na maza
A karon farko a kakar wasannin Bundesliga na maza na shekarar 2017 an samu alkalin wasa mace ta farko Bibiana Steinhaus. A gaba daya akwai wasu mata hudu a duniya da suka kai irin wannan matsayi.
Bibiana Steinhaus
Ita dai Bibiana Steinhaus sau shida tana zama Gwarzuwar shekara. A watan Mayu na shekara 2017 ta farko da ke alkalanci a wasanni Bundesliga na maza. Hukumar FIFA ta nuna cewa akwai mata hudu a kasashe daban-daban da suka kai wannan mataki a wasannin kwallon kafa na maza.
Nicole Petignat
Nicole Petignat ta na cikin mata kalilan da suka yi fice wajen alkalancin wasannin kwallon kafa na maza, inda ta yi alkalanci a wasannin lig na kasashen Sweden da Ostiriya. A 2003 ta zama mace ta farko da ta yi alkalancin wasannin cin kofin zakarun Turai, UEFA tsakanin AIK Solna da Fylkir Reykjavík. Daga shekara ta 2000 zuwa 2007 ana danganta ta da tsohon alkalin wasa Urs Meier.
Gladys Lengwe
Gladys Lengwe ta kasance alkalin wasa daga Zambiya wadda hukumar FIFA ta ce ta na zama ta farko wajen alkalancin wasannin lig na maza na Zambiya. A wasan cin kofin duniya na 2014 na FIFA, Lengwe ta sami daukaka sannan ta fara alkalancin wasannin lig na Zambiya na maza. A wannan hoton Lengwe ta na magana da tsohuwar mai horas da 'yan wasan Jamus na mata Silvia Neid a shekarar 2015.
Claudia Umpierrez
Tun shekara ta 2010 Claudia Umpierrez take alkalancin wasannin lig na wasan mata a Yurugai. Wannan kwararriyar lauya a shekara ta 2015, kamar Gladys Lengwe suka yi alkalancin wasannin kwallon kafa na duniya na mata. Tun daga lokacin sunanta yake tashe a kasashen Latin Amirka kuma ta fara alkalancin wasan lig na Yurugai a farko na maza.
Kateryna Monzul
Wata alkalin wasa wadda ta zama ta farko a kasarta da ke alkalancin wasan maza ita ce Kateryna Monzul daga kasar Ukraine. Ita dai Monzul ta fara wannan aiki tun 2004 a wasannin mata, inda ta samu daukaka har aka zabe ta a mastayin wadda ta fi hazaka a shekarar 2015. Tun shekarar 2016 ta ke alkalancin wasanni lig na maza a kasar Ukraine.