Alkalan Indiya sun soki babban jojin kasar
January 12, 2018Talla
Alkalan sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai irinsa na farko da suka kira inda su ka yi korafi kan babban Jojin kotun koli Dipak mishra cewar baya bin dokokin da aka shimfida a tsarin aikinsu, sannan yana yin yadda ya so da shari'un da aka gabatar masa. Ya zuwa yanzu dai babu wani martanin kare kai daga babban Jojin kotun kolin.
Daga bangaren Gwamnatin kasar kuwa wasu mataimakan Firayim ministan kasar Narendra Modi sun bayyana cewar yana nazarin al'amarin kuma a halin yanzu ya nemi ganawa da Manyan jami'an ma'aikatar Shari'ar kasar don nemo bakin zaren.