Jama'a na neman Abdelaziz Bouteflika ya sauka daga mulki
February 25, 2019Talla
Masu zanga-zangar wdanda tun suna karamin gungun jama'a har suka kai darurruwa sun ci gaba da yin zanga-zangar duk da yunkurin da 'yan sanda suka yi na tarwatsu da borkonon tsohuwa. Hadin gwiwar kungiyoyin farar hula wadanda ake kira Mouwatana wadanda aka girka a shekar bara domin nuna adawa da takarar ta biyar ta Abdelaziz Bouteflika su ne suka kira gangamin.