Ali Bongo ya lashe zaben Gabon
August 31, 2016Ali Bongo Odinba ya lashe zaben kasar Gabon a hukumance, da tazaran kuri'u kimanin dubu shida ne Ali Bongo mai shekaru 57 ya samu damar darewa kan kujerar shugabancin kasar karo na biyu inda ya samu kashi 49.80 cikin 100 na kuri'un 'yan kasar yayin da abokin takaransa Jean Ping ya samu kashi 48.23 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.
To sai dai tuni Jean Ping ya yi watsi da sakamakon wannan zabe, wanda hakan ya tinzira magoya bayansa suka soma zanga-zangar a ofishin hukumar zaben kasar. A tun shekara ta 2009 ne dai shugaba Ali Bongo Odinba ya dare shugabancin kasar ta Gabon bayan rasuwar mahaifinsa.
To sai dai wakilan kasa da kasa sun ja hankalin jami'an tsaro da su tsaurara matakan tsaro na ganin an takaita tashin tashina donmgudun sake jefa kasar cikin rikicin bayan zabe.