1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda: Tunawa da kisan kare dangi

Isaac Mugabi ATB, AMA
April 8, 2019

Wasu 'ya'yan da iyayensu suka hallaka sun nuna jumami kan kisan kare dangi tsakanin kabilun Hutu da Tutsi, sai dai ba dukkanin 'yan Ruwanda ba ne ke jin cewa an cimma nasarar sasantawa tsakanin kabilun.

https://p.dw.com/p/3GSc9
Ruanda 25. Jahrestag Völkermord | Zeremonie in Kigali
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya kaddamar bukukuwan mako guda na tunawa da mutane dubu dari takwas (800 000) 'yan Tutsi da 'yan Hutu masu matsakaicin ra'ayi da suka rasa rayukansu a lokacin kisan kiyashin. Matasa maza da mata 'yan shekaru 10 zuwa 12 sun rera wakokin nuna jimamin ta'asar kisan gillar da aka yi a shekarar 1994. Wasu matasan da dama kuwa sun halarci bukukuwan don samun tarihi, daga ciki har da Uwihirwe Yassipi 'yar shekaru 18 da haihuwa wadda ta ce ko da yake ba a haife ta ba a lokacin kisan kare dangin, a yanzu hakkinta ne ta shiga cikin bukukuwan alhinin domin ta jajanta wa mutanen da abin ya shafa.

Ruanda Genozid Gedenk-Zentrum in Kigali
Wata matashiya a Kigali na bayyana muhimmancin tunawa da kisan kare dangiHoto: DW/I. Mugabi

Abin da ya faru a shekarar 1994 abin takaici ne

A kasar Rwanda matasa  da dama basa iya magana game da tarihin abin da ya faru saboda tsoron kada a dauke su a matsayin wadanda ba sa kaunar shirin shugaban kasar Paul Kagame. Shugaban na Ruwanda na son kasashen duniya su yi wa batun kallo mai mahimmanci, sai dai a kasar da mazaje ke kashe matansu, makobci ya kashe makobcinsa, sasantawa tsakaninsu ba abu ne mai sauki ba, to amma kuma hukumar sasantawa da yafewa juna ta kasar ta nuna cewa kashi 95% cikin 100 na 'yan Rwanda sun yafe wa juna sun kuma manta da abin da ya faru a baya.