Alamurra na cigaba da kazanta a Iraq
August 6, 2004.:A cikin wannan artabun kuwa a yanzu ta tabbata cewa yan tawayen kasar ta iraq na cigabba da yakar dakarun kasar Britaniya da Amurka a sasan Basra da Amara baya ga Nasiriyya inda yan tawayen ke yakar sojojin Italiya .a hannu guda kuma anacigaba da dauki ba dadi a Najaf inda ake kyautata zaton cewa a kalla mutane sama da dari ukku ne suka mutu a yamutsin na kwanaki biyu .wAnnan dai shine karo na farko da yamutsin ya fiye muni tun a watan yunin wannan shekara inda aka fafata a rtsakanin magoya bayan shugaban Shaawan yankin Najef Moqtadar sadr .To sai dai kamar yarda kakakin gwamnatin kasar Gurgis Sada yace burin gwamnatin kasar ne ta kakkabe yan tawayen kasar cikin kankanen lokaci .Yace duk wata kungiyar data ki mika wuya a halin yanzu zasta kasance tamkar kungiyar yan taadda ko kuma yan tawayen dake neman haifar da zaune tsaye .Sada yace a yanzu dai duk wata kungiya dake fafutukar kare kasar ta iraq haramtacciya ce a fuskar wannan Gwambati..ya dai tabbatar da yaki ga duk wata kungiya a cikin kasar kama daga samarra Ramadi fallujah ..Tuni dai Gwamnan lardin Najaf Adnan Al zorfi ya bukaci yan tawayen Mehdi dasu fice daga birnin cikin yini guda idan kuwqa ba haka ba zasu kwashi kashin su a hannu .Yace a bisa halin da ake ciki babu wata alamar cigaba da tattaunawa domin fuskantar juna a tsakanin yan tawayen da gwamnatin lardin baki daya .a can arewacin kasar kuwa a birnin samarra da dakarun Amurka sun yi dirar mikiya a yankin tare da farautar yan tawayen dake kassara kokarin gwamnati na samun wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a kasar baki daya .Wannan samamen kuwa ya biyo bayan wani jawabi ne da ministan cikin gida na kasar yayi na cewa babu batun hawa kann teburin sulhu da yan tawayen a jiya ...a yayin da aka tambayi minisrtan cewa ko gwamnation kasar na neman cafke Moqtadar sadr a raye ko kuma a mace sai ya kada baki yace zasu cigaba da farautar kowa nene kumka komai matsayinsa a kasar matukar yana haifar da rudani a kasar .Yace tuni kungiyar moqtadar sadr ta fada sahun kungiyar yan taadda a jerin sunayen kungiyoyin yan taadda a duniya ..Bayan kwana daya da fara dauki ba dadi a cikin kasar ta iraq Amurka ta bayyana cewa a yanzu ta sanya kafar wando daya da wadanda ke garkuwqa da yan kasashen ketare a kasar .Amurka dai tace ba zata taba zama kann teburin sulhu da yan tawayen kasar ba .