Al-Shabaab ta kashe rayuka a Mogadishu
August 20, 2022Talla
Mayakan tarzoma na kungiyar al-Shabaab da ke gwagwarmaya da makamai a yankin kuryar Afirka, sun kai hari a wani babban Otel da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda rahotanni ke cewa ya salwantar akalla mutum 12.
'Yan sanda sun ce da fari maharan na al-Shabaab sun tayar da wasu nakiyoyi ne kafin su kai ga shiga Otel din wanda jami'an gwamnati da 'yan jarida da ma 'yan kasuwa ke zuwa.
Jami'an tsaron sun ce sun kubutar da wasu baki akalla 60 da yammacin jiya Juma'a lokacin da aka kai harin.
Sai dai har yanzu, akwai fargabar cewa mutane da dama na cikin ginin Otel din.