Shugaban kasar Sudan na kan hanyar komawa gida
June 15, 2015Talla
Babbar kotun Afirka ta Kudu ce dai ta bayar da umurnin dakatar da al-Bashir bayan da ta ce ta samu takardar sammacinsa daga kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata laifukan yaki, a yayin da yake halartar taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka AU a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudun. Ita dai kotun ta ICC na tuhumar Shugaba Bashir na Sudan da laifin kisan kiyashi da kuma aikata laifukan yaki a yayin rikicin yankin Darfur na Sudan din. Ana sa ran da zarar Bashir ya isa gida Sudan zai gudanar da taron manema labarai.