1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC na kokarin kama shugaban Sudan a Afirka ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 14, 2015

Shugabannin kasashen Afirka na can na gudanar da taron koli na kungiyar Tarayyar Afirkan AU a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1FgvT
Shugaban Sudan Omar al-Baschir
Shugaban Sudan Omar al-BaschirHoto: Reuters/Str

Zuwan shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir na neman mamaye zauren taron kungiyar AU bayan da wata kotu a Afirka ta Kudu - inda taron ke gudana ta bayar da umurnin dakatar da shi na wucin gadi a kasar. Dama dai Al-Bashir na daya daga cikin mutanen da kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC ke nema ruwa a jallo, bisa zargin da ake yi masa na aikata laifukan yaki a yankin Darfur na Sudan din kasar, da ya kwashe tsahon shekaru ya na mulka.

Tun da fari dai rahotanni sun nunar da cewa batun halin da ake ciki a Burundi da kuma matsalar kwararar bakin haure zuwa nahiyar Turai ne zai mamaye tattaunawar shugabannin Afirkan da ke gudana a birninJohannesburg na Afirka ta Kudu. Baya ga wannan kuma za su mayar da hankali kan batun kungiyoyin tarzoma na masu tsattsauran ra'ayi irin su Boko Haram da ta addabi Najeriya, wadannan kungiyoyi dai na neman yin aure su tare a nahiyar Afirkan.