1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AI ta zargi Kamaru da take hakkin dan Adam

Gazali Abdou TasawaJuly 14, 2016

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi kasar Kamaru da take hakkin dan Adam, ta hanyar musgunawa mutane a yakin da take yi da Kungiyar ta'addan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1JP5x
Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule
Hoto: Getty Images/Afp/Reinnier Kaze

A wani rahoto da ta wallafa a wannan Alhamis din kungiyar kare hakkin dan Adam din ta Amnesty international ta ce a kokarinta na bai wa al'ummarta kariya daga hare-haren Boko Haram kasar ta Kamaru na wuce gona da iri inda take kama mutanen da ba su ji ba su gani ba, tana tsare su a gidajen kurkuku a cikin mawuyacin hali inda ake gana masu azaba har sai rai ya yi halinsa. A cikin wata sanarwa da Alioune Tine daraktan cibiyar kungiyar ta Amnesty reshen yankin Afirka ta Tsakiya da kuma Afirka ta Yamma ya fitar kan wannan batu dai, ya ce kasar ta Kamaru ta tsare mutane sama da 1000 da suka hada har da mata a cikin halin kunci, inda da dama suka mutu a sakamakon rashin lafiya ba kulawa da rashin abinci mai gina jiki. Kungiyar ta Amnesty ta ce ta tattara wadannan bayanai ne da shaidu 29 da suka sha azaba a hannun jami'an tsaron kasar ta Kamaru tsakanin shekara ta 2014 zuwa ta 2015.