1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika ta Kudu na son ficewa daga Kotun ICC

Gazali Abdou TasawaJune 25, 2015

Matakin na a matsayin martani ne ga yinkurin da kotun ta yi na neman kama Shugaban Kasar Sudan Omar el-Bechir a taron AU na Johannesburg.

https://p.dw.com/p/1FnND
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: AFP/Getty Images/R. Bosch

Kasar Afrika ta Kudu ta ce ta soma nazarin yiwuwar ficewarta daga kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ta ICC, a wani mataki na mayar da martani ga yinkurin da wannan kotu ta yi na neman kama Shugaban Kasar Sudan Omar el-Bechir a lokacin taron Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU da ya wakana a birnin Johannesburg.

Jeff Radebe Minista a fadar shugaban kasar ta Afrika ta Kudu wanda ya bayyana wannan labari a ranar Alhamis ya ce za su shirya wani rahoto kan wannan manufa tasu wanda za su gabatar a babban taron koli mai zuwa na kotun ta ICC.

Haka zalika kasar ta Afrika ta Kudu ta ce za ta dauki duk matakkan da suka dace domin ganin an aiwatar da matakin neman yin kwaskwarima wa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Afrika wacce ke da cibiyarta a birnin Arusha na kasar Tanzaniya ta yanda za ta iya soma tafiyar da ayyukanta da hukuntar da 'yan Afrika da za a kama da aikata manyan laifuka