Afirka ta Kudu ta daukaka kara kan Omar el -Bashir
April 8, 2016Kotun ta ce a hukuncin da ta yanke mahukuntan Afirka ta Kudun na da laifi sakamakon barin shugaban kasar ta Sudan ficewa daga kasar ba tare da sun tsafke shi ba.Shugaba Omar el-Bashir wanda ya halarci taron Kungiyar AU ta Afirka a watan Yunin shekarar da ta gabata ya fice daga Kasar Afirka Ta Kudun ne duk kuwa da takardar sammacen da kotun ICC ta aike da cewar a hukumomin kasar su tsare shi.
Kotun ta ICC ta ce mahukuntan kasar kamata ya yi su kama Shugaban domin sun rattaba a hannu a kan aiwatar da duk wasu tanede-tanden kotun,to amma a nata bangaren gwamnatin Afirka ta Kudun ta ce sun bai wa dukkanin shugabanin da suka halarci taron ne kariya ta fuskar diplomasiya ne.
A yau ne dai Afirka ta kudun ta sake daukaka karar bayan da kotun kasar ta ce ta tafka kuskure kan rashin kama shugaban kasar ta Sudan.