1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: An rantsar da sabon shugaba

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2018

A wannan Alhamis aka rantsar da Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar Afrika ta Kudu, bayan da Jacob Zuma ya sanar da yin murabus a sanadiyar matsin lamba da ya fuskanta kan badakalar cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/2sim7
Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa – Vereidigung
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Tun bayan wa'adin tsohon shugaban Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela a shekarar 1999, Mandela yana da fatan ganin Ramaphosa ya gajeshi a mulki. Sai dai kutungwilar siyasa da ta dabaibaye kasar, ya disashe damar Ramaphosa da tsohon Shugaba Thabo Mbeki. Duk da cewa Mandela baya raye amma a yau za a iya cewa burin Mandela ya kai ga cika. Sai dai da alama tsugune ba ta kare ba, domin kuwa tuni manyan jam'iyyun kasar Economic Freedom Fighters EFF da kuma Democratin Allience DA sun yi Allah wadai da zaben hasali ma sun fice daga zauren majalisar yayin zaben. Jam'iyyun dai na mai bukatar a gudanar sabon zabe. 

Amma wasu 'yan Afirka ta Kudu sun yi maraba da zaben sabon shugaban Cyril Ramaphosa kamar yadda Majola me shekaru 42 ke cewa: “Na yi imanin cewa zai tabuka abin kirki, fiye da yadda ake zato. Ta bangaren tattalin arziki bamu tunanin za a yi cin hanci, shi ne mafi cancanta. Na yarda cewa zai sa mu tuna da Mandela farkon shugabanmu bakar fata.”

Shi kuwa Benjamin Matou, na bayyana ra a'yinsa da cewa: “Na yi farin ciki, Ina ganin Ramaphosa zai taka muhimmyar rawa, kuma ina da yakinin cewa yana da kwarewar da zai farfado da tattalin arzikin Afirka ta Kudu, da kuma kawata birane da samar da ayyukan yi tsakanin matasa.”

Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa – Vereidigung
Ramaphosa lokacin rantsuwar kama aikiHoto: Reuters/M. Hutchings

Wani tsohon jigo a jam'iyar ANC Dr. Makhozi Khoza da aka tilastawa yin murabus a bara, bayan da ya kalubalanci Zuma kan cin hanci, ya ce a kwai kyakkyawan fata cewa Ramaphosa zai kasance shugaba da zama abin koyi a nahiyar Afirka.

A yanzu dai baya ga hasashen makomar jam'iyyar ANC a babban zaben kasar da ke tafe, ana jiran alkalancin masana siyasa kan yadda suka auna shugabancin Shugaba Zuma. Wannan ne ma ya sa DW ta tambayi Philip de Wet dan jarida ko ya za a auna shugabancin Zuma?

"Da wuya a iya tantancewa a yanzu, amma ANC na da kyakkyawar akida da 'yan siyasa kwararru da suka ga haske a shugabancin Zuma amma a nawa bangaren bana iya cewa ga abu guda ko matsala da ya warware a matsayinsa na shugaba ba.

A ranar Juma'a ne a ke sa ran Ramahosa zai yi wa 'yan Afirka ta Kudu jawabin kasa, amma da alamar jan aiki a gabansa na warware kulli da zai iya fuskanta daga manyan jam'iyyun kasar domin ba shi damar cimma manufofinsa na farfado da tattalin arzikin kasar da maido da martabar kasar a idanun duniya.