Afirka a Jaridun Jamus(09-04-21)
April 9, 2021(Za mu fara sharhuna da labaran jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Jamhuriyar Benin inda a wannan Lahadi za a gudanar da zaben shugaban kasa. Jaridar ta ce komai tsaf a birnin Cotonou cibiyar hada-hadar kasuwancin Benin. Ta ce shekaru biyar da suka gabata aka zabi hamshakin dan kasuwa kuma mutumin da ya fi kowa kudi a Benin, Patrice Talon, mukamin shugaban kasa, inda ya yi alkawarin yinn bankwana da fadar mulki bayan wa'adin mulkinsa na farko, sai dai ya lashe amansa, domin ya sake tsayawa takara a zaben na bana, inda yake takara da mutum biyu daga bangaren adawa, wadanda ba a sansu sosai ba. Jaridar ta ce Shugaba Talon mai shekaru 62 a duniya, ya kawo ci-gaba a Kasar ta Benin, musamman birni Cotonou inda aka sabunta wurare masu yawa. Sai dai kusan ba a jin duriyar 'yan adawa a fagen siyasar kasar da ke yammacin Afirka. Wani sabon tsarin zaben kasar ya kawo babban cikas ga sanannun 'yan adawa da aka haramta musu yin takara.
Kamfanin Total a dakatar da aikin da yake a Mozambik saboda hare-hare na 'yan taadda
Kamfanin hakan man fetir na Total, mallakin kasar Faransa ya dakatar da babban aikin da yake yi a kasar Mozambik saboda hare-haren 'yan bindiga masu kishin addini, wannan shi ne taken labarain da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga, inda ta mayar da hankali kan tabarbarewar lamarun tsaro a arewa maso gabashin kasar Mozambik. Kamfanin na Total ya dauki wannan mataki ne bayan da wasu gamsassun bayanai suka ce kungiyar 'yan tawayen Ahlu Sunna wal Jama'a da baya-bayan nan ta tsananta kai hare a Mozambik, tana dannawa kusa da wurin da Total ke aikin hakan iskar gas da ke a yankin Afungi. Mahakan iskar gas din dai na kusa da birnin Palma mai tashar jiragen ruwa da ke zama matattarar hada-hadar gas, inda a karshen watan Maris mayakan kungiyar suka fara kai hari kan birnin mai yawan al'umma dubu 75. Farar hula da yawa da 'yan sanda da dakarun tsaro na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren. Ita ma jaridar Die Tageszeitung ta yi sharhi kan halin da ake ciki a birnin na Palma, inda ta ruwaito masu tserewa daga birnin na cewa 'yan bindiga sun kashe birnin. Sai dai jaridar ta ce sojojin Mazambik sun sake kwace birnin daga Musulmi 'yan tawaye. Amma an ragaza birnin, dubban mutane sun gudu, suna kuma cikin mawuyacin hali babu kariya babu wani taimako. Jaridar ta jiyo wata kafa na cewa akwai mayakan kasashen ketare musamman daga Tanzaniya da wasu kalilan daga Afirka ta Kudu a cikin kungiyar ta Kasar Mozambik.
Basussuka sun yi wa Zambiya katutu wanda ta gaza biya sakamakon matsi na tattali arziki saboda corona
A karshe za mu leka kasar Zambiya wadda a cewar jaridar Neues Deutschland, tattaunawar da ake da ita a kan basussukan da suka yi mata katutu, na cikin sarkaiyar gaske saboda mabambantan kafofi da suka ba ta bashi. Asusun Lamuni na Duniya da bankuna masu zaman kansu da cibiyoyin hada--hadar kudi na kasar China na daga cikin wadanda suka ba wa kasar bashi. Zambiya wadda ta dogara da cinikin albarkatun karkasin kasa kamar tagulla don samun kudaden musaya a ketare, annobar corona da faduwar farashin kaya a kasuwannin duniya, sun jefa kasar cikin wani yanayi da ba za ta iya biyan kudin ruwa balantana uwar kudin kanta ba. Duk wata tattaunawa da nufin kawo mata sauki tana cikin rashin tabbas saboda kafofi mabambanta da suka ba ta bashin.