Afirka a jaridun Jamus 02.08.2024
August 2, 2024Guinea ta kafa tarihi a bangaren shari'a "wannan shi ne taken labarin da jaridar die Tageszeitung ta wallafa dangane da hukuncin daya daga cikin laifukan kisan kiyashi mafi girma da mulkin kama-karya na soji ya yi a Afirka.
Jaridar ta ci gaba da cewa, wata kotu ta musamman a kasar Guinea ta yanke wa manyan wadanda ake tuhuma da laifukan cin zarafin bil adama, hukunci. A daidai lokacin da za a yanke hukunci mai cike da tarihi, jandarmomi dauke da manyan makamai ne suka mamaye dukkan kofofin shiga kotun a ranar Laraba, inda aka yanke wa tsohon shugaban mulkin soja Moussa Dadis Camara mai shekaru 59 da haihuwa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 20 saboda laifukan cin zarafin bil Adama da ya aikata da mukarrabansa. Zaman sauraron shari'ar dai an watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar ta Guinea.
Ba kasafai tsofaffin shugabannin mulkin sojan su kan amsa da kansu a gaban kotu a kasarsu ba, a kan irin laifukan da suka tabka a lokacin mulkinsu. Manyan wakilan kungiyoyin kare hakkin bil'adama daga ko'ina a duniya da ma babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya sun yi tattaki zuwa babban birnin kasar Guinea, watau Conakry lokacin da aka gudanar da wannan shari'a. Tuni dai lauyoyin da ke kare masu laifin suka ayyana daukaka kara.
"An kashe sojojin Wagner a Mali" shi ne taken sharhin jaridar Berliner Zeitung a kan harin sojoji da 'yan tawayen Abzinawa suka dakile a Mali.
Jaridar ta ce Mali da kawayenta na Rasha sun fuskanci koma baya a bangaren soji. A wani kazamin fada da aka gwabza a arewacin kasar, 'yan tawayen Abzinawa sun yi ikirarin samun galaba a kan sojojin Mali da sojojin Wagner na Rasha.
Tun a shekara ta 2021 ne dai sojojin hayar ta Wagner da takwarorinsu na Mali ke yakar kungiyoyin masu tada kayar baya da ke arewacin wannan kasa da ke yankin Sahel, ciki har da mayakan ta'addanci na Islama da Abzinawa.
Majiyoyin Rasha na kusa da sojojin hayar da suka hada da tsohon kwamandan sojojin da ke arewacin Mali, sun tabbatar da kashe mayakan da kuma sojojin na Wagner, daura da wadanda suka jikkata, baya ga Abzinawan da suka yi awon gaba da wasu jami'ai.
Za mu karkare shirin na wannan makon da labarin jaridar Der Tagesspiegel a kan halin da ake ciki a rikici mafi muni a Afirka watau rikicin kasar Sudan, kasar da miliyoyin al'umarta ke cikin halin kaka ni kayi na rayuwa. Jaridar ta ci gaba da cewa, daya daga cikin manyan bala'o'in jin kai na duniya yana faruwa a Sudan.
Mutane miliyan tara ne ke gudun hijira, kashi 53 cikin 100 na wadanda suka rasa matsugunansu ‘yan kasa da shekaru 18 da haihuwa ne. An katse hanyoyin samar da kayan agaji, mutane miliyan biyar ne ke fuskantar barazanar yunwa da mutuwa.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023 ne dai yaki ya barke kan madafan iko tsakanin sojoji kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun sa kai na RSF karkashin Janar Mohamed Hamdan Dagalo. A makon da ya gabata ne Amurka ta gayyaci bangarorin biyu da ke gaba da juna a tattaunawar da za a fara ranar 14 ga watan Agusta a kasar Switzerland. Sai dai akwai a yar tambaya dangane da wannan yunkuri, tun bayan tsallake rijiya da baya da Janar Burhan yayi a wani harin jirgi mara matuki a ranar Laraba a yankin gabashin kasar.