Mutum 15 sun mutu a yunkurin neman visa
October 21, 2020Talla
Yan kasar Afghanistan kimanin goma sha biyar ne suka rasa rayukansu a sanadiyar cunkoson da aka samu a kusa da ofishin jakadancin kasar Pakistan da ke kasar, goma daga cikin mamatan mata ne sauran kuma tsofaffi.
Rahotanni sun ce, lamarin ya auku ne a yayin da mutum sama da dubu uku, ke rige-rigen bin layi don samun takardar visar shiga kasar Pakistan. Kawo yanzu dai babu karin haske daga jami'an ofishin jakadancin na Pakistan a game da lamarin.