Adadin wadanda suka rasu a sansanin Dikwa ya karu
February 11, 2016Babban jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya ya tabbatar da wannan adadi, inda ya ce a halin yanzu wadanda suka jikkata na can suna samun kulawa a asibitoci. 'Yar kunar bakin waken ta uku dai ta ki amincewa ta tayar da bam din da ke jikinta, bayan da ta yi la'akkarin cewa a kwai uwayanta da sauran danginta cikin wannan fili, inda daga bisani ta mika kan ta ga hukumomi.
Akwai dai sama da mutane dubu hamsin da ke zaman gudun hijira a wannan sansani kuma yawancin su sun fito ne daga kanan hukumomin Ngala da Kala Balge da Dikwa da Mafa da Marte da karamar hukumar Bama duk a jihar Borno. Wadan nan sabbin hare-hare na tayar wa mazauna yankin hankali a lokacin da suka fara sakin jiki tare da fatan da suke na komawa garuruwan su ba da dadewa ba.