Abin kunya a Najeriya tattare da rarar kudin man fetur
April 24, 2012Daga dukkan alamu dai babu alamar tsoro a cikin zuciya da aiyyukan da suke shirin aiwatarwa.
Kuma akwai alamun shiri da ma kokari na hadin kai a tunanin yayan majalisar wakilan tarrayar Najeriya da suka ma manta da batun ra'ayi ko banbanci na siyasa waje tunkarar zargion sama da fadin dubban miliyoyin nairorin da ake yiwa kamfanin man kasar na nnpc da ma raowar wasu yan uwansa 70 da suka taka rawa a cikin badakalar tallafin man fetur din da ta nemi tsaida alamuran kasar ta Najeriya a farkon shekarar da muke ciki.
Tun da farkon fari dai shi kansa shugaban majalisar da a baya yasha hasashen fuskanatar barazanar tsigewa ya karya kummalao ada wani jawabin dake kalubalan bangaren zartarwar kasar na farkawa da nufin tunkarar annobar cin hancin da ke zaman rowan dare da kuma ke barazana ga cigaban tarrayar Najeriya
Jawabin kuma da ya sha tafi da guda daga wajen yan uwansa yan majalisar a wani abun dake zaman alamu na magani da yawu iri daya kan batun day a tada hankula kuma ke zaman badakala mafi girma a cikin tarihin demokaradiyar kasar ta Najeriya.
Kafin daga baya kuma aka kaddamar da muhawarar dashi kansa shugaban kwamaitin bincike ya dauki tsawon kusan mintuna 30 yana zayanna dalla dallar badakalar da suka dago da kuma dalilin sun a kawo shawarwari dai dai har 62 da a cear sa aiwatar dasu ke iya kaiwa ga tantance aya da tsakuwa r rikicin man fetur din kasar ta Najeriya.
Babu dai wata doguwar muhawara a tsakanin yan majalisar da suka rika bi suna bayyana yardarm su da kusan dukkanin shawarwari kwamitin da suka hada da kaddamar da cikakken binciken hukumomin yaki da cin hancin kasar kan hukumomin dake da ruwa da tsaki da batun na tallafi da kuma karkasa kamfanin man kasar na nnpc ya zuwa gida gida tare da dauke shugabancin zartarwarsa a hannun ministan man fetur din kasar ta Najeriya.
Kwaimtin ya kuma Ambato wasu kamfanoni 15 da suka karbi kudin na tallafi har kusan naira miliyan dubu65 ba tare da samar da ko da digo na man fetur din bad a kuma wasu da sukaci naira miliyan dubu 41 amma suka ki bayyana a gabansa, banda kuma wasu jerin 71 da akayiwa aringizon kusan milliyan dubu 230.
Ana dai kallon rahoton kwamitin a matsayin sabon babi ga kokarin tunkarar matsalar cin hanci da rashawa da ma halin bera irin na wasoson dake zaman rowan dare a tsakanin yan kasuwa da masu siyasar kasar ta Najeriya.
To sai dai kuma an sha ruwa kasa tana shanyewa a tarrayar Najeriya inda bincike ke zaman ado, amma kuma hukunta masu laifi ke karanci a tsakanin shugabannin dake tafi da harkokin kasar abun kuma da a cewar hon Garba Datti dake zaman dan majalisar daga jihar Kaduna ya kama hanyar sauyawa.
Tuni dai shi kansa kamfanin man kasar na NNPC ya kira rahoton kokarin son rai irin na majalisar kasar, sannan kuma wasu daga cikin kamfanonin ke shirin zuwa kotu da nufin hana aiwatar da sakamakon sa.
A wani abun dake nuna jan aikin dake tsakanin yan majalisun da kuma koakrin ganin bayan halin beran kasar ta Najeriya da kila ma fito na fito a tsakanin yan majalisar da bangaren zartarwar kasar
Hon. Musa Sarkin Adar dai na zaman dan majalisar daga sokoto.
Abun jira a ganio dai na zaman matakin gwamnatin kasar da har ya zuwa yanzu tai na kurma game da rahoton dake iya shafar manyan jiga jigan yayan jamiyyar PDP mai mulkin kasar ta Najeriya na lokaci mai tsawo.
Hon Garba Di dai na zaman dan majalisar daga jihar Kaduna.
To sai dai kuma babban matsala na zaman makomar rahoton da tuni ya fara tada kuri a sassa daban daban na tarrayar najeriyar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu