A ƙasar Saliyo zaɓen shugaban ƙasa ya bar baya da ƙura
November 28, 2012Yan adawa Saliyo sun yi ƙira ga magoya bayansu da su ƙaurawa cewa ofisoshin gwamnati, bisa abinda suka ƙira tabka maguɗi a zaben shugaban ƙasa da ya gabata. Jam'iyar SLPP tace tana yin kira ga zaɓaɓɓun yan majalisa da shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolinsu, duk su ƙauracewa ofisoshinsu, har sai abinda hali ya yi. Zaɓen ranar 17 ga watan da muke ciki ya sake maida shugaba Ernest Bai Koroma kan mulki a wani wa'adi na biyu, bayan ya samu kashi 58 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar. Babban mai ƙalubalantansa, Julius Maada Bio ya biyo shugaban a baya da kashi 37 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa. Wannan dai ba shine karon da jam'iyar adawan ke ƙauracewa zaman majalisa ba, inda ta yi hakan a watan jiya bayan wata taƙaddama da jam'iyya mai mulki.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal