A Nijar an sake kama matar Hama Amadou
May 31, 2017Talla
Tun farko an yanke wa mutane guda 20 hukuncin daurin zaman yari na shekara guda a cikin watan Maris da ya gabata saboda cikin jarirai kafin a sallame su daga baya. A yanzu an tisa keyar su zuwa gidajen kurkukun domin idasa hukuncin da aka yanke musu na zaman gidan yarin. Su dai matan an kai su ne gidajen kurkuku na Kolo, yayin da su kuwa mazan aka kai su gidajen kurkuku na Say.
Yau dai sama da shekara guda ke' nan da tsohon kakakin majalisar dokokin Nijar Hama Amadou ke zaman hijira a Faransa, bayan zaman kason watanni hudu da ya yi saboda laifin cinikin jariran, kafin daga bisani ya fice hijira a Faransar, saboda dalilai na rashin lafiya.