A naɗa sabuwar shugabar asusun IMF
June 28, 2011Talla
Kwamitin Zartaswa na asusun bada lamuni na duniya ya zabi Christine Lagarde ministan tattalin arziki ta ƙasar Faransa a masayin sabuwar shugabar Asusu IMF.
Lagarde yar shekaru 55 da haifuwa ta kasance macce ta farko da zata riƙe muƙamin bayan da tsofon shugaban hukumar Dominique Strauss Khan wanda ke fuskantar tuhuma a gaban shara'a kan laifin yin fayɗe ga wata matar mai yin shara a Hotel a Amurka ya yi marabus.
Tun can da farko dai masu aiko da rahotannin sun ce zaɓin na Christine ba zai samu wata jayaya ba bayan da ta samu goyon bayan Amurka a gaban ɗan takarar ƙasar Mexiko.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad tijani Lawal