SiyasaAsiya
A Alhamis din nan ne kotun ICC za ta yanke hukunci kan Syria
November 16, 2023Talla
A Alhamis din nan ne kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague wato ICC, za ta yanke hukunci kan zargin take hakkin bil Adama da ake yi wa kasar Syria, sakamakon yadda bincikenta ya gano cewa an kashe dubban fararen hula tun bayan fara yakin kasar a shekarar 2011.
Karin bayani:Assad a taron kungiyar kasashen Larabawa
Kasashen Canada da Holland ne dai suka bukaci kotun ta gaggauta daukar matakin kawo karshen muzguna wa 'yan adawar kasar a kurkuku da gwamnatin Bashar al-Assad ke yi.
Karin bayani:'Yan Siriya na zanga-zangar kin al-Assad
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Faransa ta ayyana izinin kamo Shugaba Bashar al-Assad, bisa zargin tauye hakkin 'dan Adam ta hanyar amfani da guba a shekarar 2013.